Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce cikin ko wadanne mutane 10 da ake da su a duniya, 9 na shakar gurbatacciyar iska abinda ke kai ga mutuwar mutane sama da miliyan 6 kowacce shekara.
Nan gaba kaɗan ne cikin watannan shugabannin ƙasashen duniya za su taru domin tattauna matakan kare ɗumamar yanayi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi da za a gudanar a ƙasar Masar.